Share this on:
 • 25
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  25
  Shares

Dadin kowa episode 90

A cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 90 zaku ga yadda take kayawa a gidan malam Musa tsohon soja biyo bayan batan dabon da kudin da ya baiwa baraka ajiya sukayi, ko za’a gano wadannan kudade.

Ta tabbata malam Ayuba mai gadi ya gama kamuwa sosai a soyayyar Hannatu yar wajen Kamaye awon igiya, duba da irin yadda yake ta kara kashe mata zunzurutun kudi ita da mahaifiyar ta Adama. Sai dai da alamu Kamaye ya kusa gano halin dw ake ciki. Ko zai aminta da wannan hadin?

Da alamu dai DanBaba dan wajen Alhaji Buba ya samu sabuwar hanya da zai cigaba da sheqe ayarsa ta ita duk da cewa an kawo shi gidan malam Nata’ala ne don ya gyaru ya zama mutum nagari.

Soyayyar Ibrahim IB da Bintu kullum sai kara girma take yi. A bangare daya kuma, Yasmin na kokarin ganin cewa ta mayar da Bintu zuwa rayuwar shaye-shayen wacce IB ya haneta da ita. Ko yaya zata kaya?

Wadannan dama wasu sauran batutuwan na nan a cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo kashi na 90.

Ku sauke wannan bidiyo daga tashar YouTube ta gidan talabijin din tashar Arewa24 dake kasa

Dadin kowa sabon salo episode 90


Share this on:
 • 25
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  25
  Shares