Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A cikin wannan shiri na dadin kowa sabon salo episode 91 zaku ga halin da Madam Gloria take shirin shiga tun biyo bayan da Samuel ya bukaci ta tattaro mishi duka kudin shi dake hannun ta wanda har ta kai ga ya fara yi mata barazana da rayuwarta.

A bangare guda kuma, soyayya sai kara karuwa take yi tsakanin IB da yar uwarsa Bintu. IB ya bukaci Bintu da ta rabu da kawarta Yasmin duba da cewar zata iya maida ta rayuwarta ta baya.

Rayuwa sai kara yi wa Stephanie da mahaifinta Daniels tsauri take tun bayan da suka rabu da Madam Gloria, wanda har ta kai ga abinci da zasu ci yana neman ya gagare su.

Da alamu dai DanBaba ya samu ya kubuce daga gidan malam Nata’ala, ko yaya zata kaya tsakanin Malam da Alhaji Buba.

Wadannan dama wasu sauran batutuwan na nan a cikin shirin dadin kowa sabon salo episode kashi na 91

Dadin kowa sabon salo episode 91


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •