Tashar arewa24 taci gaba da daukar shirin wasan kwaikwayon nan mai kayatarwa na dadin kowa amma da wasu sabbin fuskoki da yan sauye-sauye wanda saboda haka ne ma su ka lakaba masa suna Dadin kowa sabon shiri.

A cikin wannan sabon shirin zaku ga yadda gimbiya da yar uwarta sa’adatu ke rayuwa tare da begen sake ganin Alawiyya da yan uwanta Bintalo da Kande. Koda yake Gimbiya ta fidda ran sake ganin Alawiyya a rayuwarta.

A wani bangaren kuma, halin kunci da babu sun dami iyalan malam Ayuba, a yayin da shi kuma yake zagayewa ya fita waje ya ci abinci me rai da lafiya.

Sannan kuma zaku ga dawowar sallau garin dadin kowa a firgice wanda hakan yasa ake mashi kallon mahaukaci.

Zakuga yadda ta kaya tsakanin malam Hassan mai sittin da kuma malam Tanimu biyo bayan almajirai da ya kawo makarantarsa.

Gimbiya ta yanke shawarar zuwa gidan su Haidar don taji yaya matsayin alaqarsu a yanzu….

Ga wasu daga hotunan wannan sabon shiri na dadin kowan tashar Arewa24

Dadin Kowa Sabon Shiri

Dadin Kowa Sabon Shiri

Dadin Kowa Sabon Shiri

Dadin Kowa Sabon Shiri

Dadin Kowa Sabon Shiri

Dadin Kowa Sabon Shiri

Dadin Kowa Sabon Shiri

Dadin Kowa Sabon Shiri

Dadin Kowa Sabon Shiri

Kamar dai yadda aka saba, za’a rika sakin wannan wasan kwaikwayo a duk karshen mako.

Ku kalli wannan sabon shiri daga Rumbun bidiyon youtube na tashar Arewa24