Share this on:
 • 20
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  20
  Shares

Shahararren jarumi kuma fitaccen mai shirya gami da bada umarni a masana’antar kannywood Haruna Talle Mai fata ya bayyana dalilin da ya janyo ra’ayin shi zuwa shiga harkar film din Hausa. Jarumin ya bayyana nasorinsa a wannan masana’anta.

A hirar shi da jaridar Daily Trust ta karshen mako, jarumin ya bayyana yadda akayi ya fara harkar film har zuwa matakin da yake yanzu.

“Dalin da yasa na tsunduma harkar film shine yanayin yadda yan film ke burgeni ta hanyar yadda suke mu’amala da mutane, ko ina ana basu girma, ana mutuntasu kuma ganin yadda mutum zai yi suna duniya ta sanshi.”

“Da farko na fara samun dan uwana Baban Umma Talle Maifata, wanda ya kasance mai shirya shirin(producer) ne a wannan lokaci domin ya sanya ni cikin harkar, to amma sai naga ya dade bai sani ba ni kuma sai nayi fushi na dauki gabarar shiga kannywood da kaina. “

“Da farko na fara haduwa da Bello Muhammad Bello (BMB), inda naje masa da wani film (zuciyata) da na rubuta sai na bashi ya duba sannan ya amince muyi aiki tare. Film din ya samu karbuwa sosai daga wajen masu kallo.”

Da aka tambayi jarumin kan cewar ko yana fuskantar wani kalubale a gidan shi dangane da harkar film da yake, duba da yadda jarumai da yawa ke fuskantar matsaloli da matayen su? Sai ya kada baki yace:

“Ina da abokanen aiki mata da yawa wanda yawan su ya kusan ya zarta yawan abokanen aiki maza da nike dasu. Hakanan a bangaren masoya na ma, ina da masoya mata da yawa, amma ko kadan hakan bai taba haifar min da wata matsala tsakanina da matata ba; saboda ta yarda dani sosai.”

“Mata ta aminta da ni sosai saboda bana boye mata komai a harkokina, hatta kalmar sirrin (password) wayoyi na ba wacce bata sani ba. Kuma nakan bar waya ta a gida da gangan don ta bincika.”

“Akwai lokuta da dama da nakan kai jarumai mata gidana su kwana in muna daukar film a cikin Jos, wanda matar tawa ita kan yi musu girki su ci, kuma ta gamsu da hakan”

“in takaice maka bayani, yanzu haka ma matar tawa ta fara shirya gami da bada umarnin film, inda take samun yan kudaden da take yin hidimomin gabanta da su.”


Share this on:
 • 20
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  20
  Shares