Fitaccen jarumin nan na wasan kwaikwayon Hausa da turanci wato ta Kannywood da Nollywood Ali Nuhu Muhammad ya bayyanawa dalilin da yasa ya yanke shawarar fara fitowa a cikin fina-finan barkwanci da a da ba’a saba ganin shi a ciki ba.

ali-nuhu-kanwar-duba-rudu
Photo: Ali Nuhu da Rahama Sadau, Kanwar Duba rudu

Jarumin dai ya bayyana cewa ya yanke shawarar yin hakan ne domin ya bayar da gudummuwar sa a wannan bangaren sannan kuma ya sake fuskantar wani sabon kalubalen don kuwa ya gaji da yadda ya dauki tsawon lokaci yana fitowa a matsayin saurayi yana ta tikar rawa.

Jarumin dai yayi wannan batu ne a yayin firar sa da tashar tauraron dan adam din nan ta Arewa24 a makwanni biyu da suka gabata a yayin da ake daukar shirin nan nasu na Kundin Kannywood.

Haka zalika ma dai jarumin ya musanta zargin cewa sun kanannade harkar fim din inda sukan hana sabbin fuskoki fitowa domin su taka irin tasu rawar inda ya bayyana cewa masana’antar shirya fim din tana da fadin gaske da wani ba zai iya tarewa wani wurin sa ba.