Share this on:
 • 36
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  36
  Shares

Fitacciyar jarumar nan ta wasan kwaikwayon Hausa ta Kannywood Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da suna Hadiza Gabon ta bayyana dalilinta na yanke shawarar fara fitowa a film din kudancin Nigeria wato Nollywood.

A wata hira da wakilin BBC Nasidi Adamu Yahaya, jarumar ta bayyana dalilinta na fitowa a fina-finan Nollywood don kawai ta gwada sa’arta da basirar da Allah ya bata wajen fitowa a wasan kwaikwayo a wurare dabam-daban.

Jarumar tace “Ba wannan ne karon farko da na soma yin film da turanci ba. Lokacin da na je Amurka, na fito a wani gajeren film na turanci, amma dai wannan shine karon farko da na fito a fina-finan Nollywood.

“Shaharenren jarumin masana’antar fina finan ta Nollywood Mike Ezuruonye ne ya gayyace ni na fito a wani film dinsa mai suna ‘Lagos real fake life’.

“Shi ne producer na film din kuma na fito ne a matsayin ‘yar arewa. Zan rika yin shiga irin ta ‘yan arewa don haka irin kayan da nake sawa a fina-finan Kannywood irinsu nake sa wa a wannan film”.

Jarumar ta kara da cewa “Tun da ya gaya min cewa zai so na fito a film dinsa, na shaida masa cewa ba kowacce rawa zan taka ba. Bazan fito a matsayin da zai sabawa addinina ba ko kuma al’adata”.

Hadiza Gabon ta ce babu wani “bambanci tsakanin yadda ake yin fina-finan Nollywood da na Kannywood idan ban da bamabancin harshe. Don haka na ji dadi dana fara fitowa a fina-finan Nollywood”.


Share this on:
 • 36
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  36
  Shares