Sarkin Kannywood wato jarumi Ali Nuhu Muhammad ya bayyana matakan da yake bi wajen samun nasarori a cikin lamurransa na harkar fina-finai. Ya kuma bawa matasa masu tasowa shawara akan suma suyi amfani da wadannan matakai don kaiwa gaci.

Ali Nuhu 2018

Jarumin yayi wadannan jawabai ne dai a cikin wani dan gajeren video nashi na sabuwar shekara da ya wallafa a shafinsa na sadarwar zamani ta Facebook.

“A matsayina na wanda ya dade a wannan masana’anta nakan bada shawara akan mutum ya kasance ya zama mai jajircewa wato rike aiki ba wasa wannan yana daya daga cikin hanyoyi da mutum zai bi wajen ganin cewa ya kai ga gaci akan sana’ar da yake ko wacce iri ce.”

“Duk damar da Allah ya baka ya kamata kayi amfani da ita. Yanzu ina magana ne akan jajircewa wajen matasa masu tasowa to wannan yana daga cikin irin sirrin abinda nake. Ina da jajircewa akan sana’ata. ”

“Sannan kuma ana cewa farar aniya laya, idan kaga wata dama wadda ba lallai dole sai kai ba, na wani ko na wata da zaka iya taimaka musu ya kasance sun tsaya da kafarsu to ya kamata ace mutum yayi kokari yaga cewa ya bawa mutumin nan hadin kai saboda shima ko ita su samu su kafu.”

“Duk ina ganin wadannan abubuwan suna daga irin abubuwan da yasa alhamdulillah a baya har ya zuwa yanzu muna da yan uwanmu da kuma abokan mu da muke cikin masana’antar gaba daya. ”

Ads