Share this on:
 • 52
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  52
  Shares

Jarumar fina-finan Hausa, Hauwa Abubakar
wacce aka fi sani da Hauwa Waraka, ta ce tana
yawan fitowa a mutuniyar banza ne saboda ta
nunawa al’umma illar rashin kirki.

“Ina fitowa a matsayin karuwa ko ‘yar kwaya ko ballagaza ne saboda na ilimantar da mutane domin su guji zama irin wadannan mutane”, in ji Hauwa Waraka,

Ta kara da cewa, “Ban taba karuwanci ba kuma ban taba yin hulda da karuwai ba, amma idan ina taka rawa a matsayin karuwa kai ka ce ni tsohuwar magajiya ce.”

A cewar jarumar bai kamata mace da za ta fito a matsayin karuwa “a gan ta sanye da hijabi ba. Ko kuma macen da ta fito a matsayin ‘yar shaye- shaye a gan ta ras kamar mutuniyar kirki ba.

“Shi ya sa za ka gan ni ina keta rashin mutunci a fim kamar da gaske. Kuma abin da ya kamata
kenan.”

Hauwa Waraka ta ce sau da dama tana zuwa
unguwa mutane suna “cewa wacce irin kwaya ko wiwi ko taba za su kawo min na sha. Ba su san cewa ban taba shan kayan maye ba; wallahi ko taba ban taba sha ba. Duk abin da ka ga ni a fim ne”.

Da aka tambaye ta kan zargin da ake yi wa ‘yan fim na luwadi da madigo, jarumar ta ce akwai
bara-gurbi sosai a cikinsu “kamar yadda akwai su a cikin ko da Malaman addini amma bai kamata a yi mana kudin-goro ba.”

Ta bukaci mutane su rika yi musu uzuri
musamman ganin cewa su ma mutane ne kamar kowa.


Share this on:
 • 52
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  52
  Shares