orlando-us-night-club-shooting

A yaune wani dan bindiga da ake alakantawa da kungiyar yan ta’adda ta IS ya harbe mutane akalla 50 tare da jikkata wasu 53 inda daga bisani shima ya rasa ransa a harbe-harbe da sukayi da jami’an tsaro.

Wannan lamarin dai ya faru ranar lahadin nan a wani gidan cashewa na yan luwadi dake Orlando, a yankin Florida na kasar amurka.

Shugaba Obama ya bayyana wannan hari a matsayin mafi muni a ciken hare-hare da yan bindiga ke kaiwa a tarihin kasar.

Hukomomin tsaro na kasar Amurka sun bayyana sunnan wannan dan bindiga da Omar mateen wanda suka ce haifaffen Amurka ne amma iyayensa yan asalin Afghanistan ne.

Hukumomin sun kara da cewar sai da maharin ya kira 911 inda ya sanar dasu cewa shi magoyin bayan kungiyar IS ne kafin daga bisani yaje ya aiwatar da wannan danyen aiki..

Luwadi dai wani abune da wasu addinnan suka haramta gami da hukunci mai tsanani ga wadanda aka samu suna aikata hakan.

Tura wannan labari zuwa abokanka…