Share this on:
 • 8
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  8
  Shares

Adekunle Silas, matashi dan shekara 26 shine wanda ya assasa kamfanin “Reach Robotics” wanda yanzu haka shine kamfanin da ya fara hada manhajar wasanni (game) kayatacciya ta “robot”, inda yanzu haka yake mazaunin masanin kimiyar “robot” mafi tsada a duniya.


Adekunle Silas

An haifi Silas a birnin Lagos inda ya girma har ya fara karatu kafin daga bisani ya koma kasar Ingila(England) tare da iyayenshi inda yayi karantun sakandiren shi a can, sannan kuma ya samu takardar zuwa Jami’ar “West Of England” inda ya kammala karatun shi da daraja ta farko (1st class) a bangaren “Robotics”.

A shekara ta 2013 ne dai Silas ya assasa kamfanin “Reach Robotics” wanda a cikin shekara hudu ya kara samu ilmi mai dimbin yawa gami da kara gogewa sosai a bangaren aikin “robots” din.

A shekarar 2017 ne Adekunle Silas ya kaddamar gami da fara fitar da manhajar wasa(game) ta robot da ya yiwa lakabi da “Mekamon” wacce ta samu karbuwa sosai, domin ko sai da aka siyar da akalla guda 500 wanda kudinsu yakai kimanin $7.5(N2.6billion).

Biyo bayan wannan gagarumar nasara, Silas ya samu karin tallafi daga kafofi da dama, ciki harda “London Venture Partners” wadanda suka bashi $10(N3.5billion). Bayan nan ne silas ya kulla huldar kasuwanci da shahararren kamfanin kimiyya wato Apple wanda hakan ya kara daga masa kasuwar kayan sa.


Share this on:
 • 8
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  8
  Shares