Share this on:
 • 16
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  16
  Shares

Engineer Yakubu Nuhu Danja, dan takarar da ya lashe zaben fitar da gwani na dan majalissar tarayya mai wakiltar Bakori da Danja a karkashin jam’iyyar APC ya koka dangane da yunkurin sauya sunan sa da ake yi da na wani dan takarar.


Kamar dai yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito, Yakubu Danja ya doke abokin karawarsa wanda shine dan majalissa mai ci a yanzu, wato Hon. Amiru Tukur Idris Bakori da kuri’a 314 a yayinda shi kuma yake da kuri’a 305, wanda hakan yasa kwamitin shirya zaben APC ta kasa reshen jahar Katsina ta hannun Dr. Isah Adamu tabbatar ma da Engineer takarar wannan kujera.

Ya kara da cewar dukda kokarin da Gwamnan jahar Katsina Hon. Aminu Bello Masari da kuma shugaban jam’iyyar APC na jahar Katsina keyi wajen ganin sun daidaita lamuran amma abin na neman yafi karfinsu saboda wasu ne daga Abuja ke yunkurin murde zaben.

Daga karshe Dan takarar yace lokacin da hukumar zabe ta bada wajen mika duk wasu sauye-sauye na kara kurewa. Idan ya kasance ba’a dauki matakin gyarawa ba, to ba shakka zai shigar da kara kotu.


Share this on:
 • 16
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  16
  Shares