Sakamakon halin da kasa ta shiga na rugujewar tattalin arziki yasa kamfanin Dangote group ya rage farashin siminti daga naira 1800 zuwa 1300.

Sanarwar na zuwa ne bayanda kamfani ya bude wasu sabbin rassa guda biyu a jihar Edo da kuma jihar Osun dake kudancin kasar nan.

Yayin da yake jawabi a Umahia , darektan kula da kamfanonin Dangote cement na yanki kudu maso yamma Johnson Olaniyi ya bayyana cewa suna nan suna iya bakin kokarinsu don inganta laushi da saukin aiki wajen simintin nasu.

Ya bayyana cewa rashin siminti mai inganci ka iya kawo saurin rushewar gine-gine. Daga nan ne ya bayyana labarin rage farashin buhun simintin..