Fitaccen jarumin nan na masana’antar fina-finan hausa ta Kannywood Aminu Sheriff yayi karin haske game da kalubalen da masana’antar ke fuskanta tare da hanyar da za’a bi wajen samun cigaba.

Aminu Sheriff wanda aka fi sani da Momoh yayi wannan karin haske ne a hirar shi da sashen Hausa na BBC.

“Babban kalubalen da muke fuskanta shine a samu manufa daya ko wata taswira da za a shata domin kai masana’antar Kannywood ga ci gabanta da kuma bunkasar harshen Hausa.

“Idan za a ci gaba da yin fina-finan da ba su da al-kibla, babu inda za a kai. idan ba za mu iya yin hakan ba, babu riba a harkar Kannywood.” in ji jarumin.

Jarumin wanda ya lashe kyautar gwarzon shekara ta City people awards ya wanzar da kanshi game da zargin da ake mashi na cewa ya tozarta wata jaruma a shirin Kundin kannywood wanda yake gabatarwa a gidan telebijin na Arewa24.

Yace yayi wa jaruma Umma Shehu tambaya kan addini bayan ta sanar mashi da cewa bata cika samun lokacin kallon fina-finai domin mafi yawanci tana zuwa makaranta ne.

“Abin da ya sa na yi mata tambaya kan addini shi ne, na ga ana yawan yabawa ‘yan fim maganganu cewa ba sa zuwa makaranta, ba su da ilimi musamman na addini ballantana na boko.”

“Da na ji ta ce ba ta damu da kallon fim ba saboda tana zuwa makaranta sai na samu karsashin nunawa masu yi mana irin wancan kallo cewa ‘bari na tambaye ta kan addini domin ta nuna musu cewa ba duka aka taru aka zama daya ba’.

“Kuma ina ganin fahimta ce mutane ba su yi ba shi ya sa suke ganin kamar ba ta amsa tambayar da na yi mata ba” , in ji jarumin.

Ads