Share this on:
 • 230
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  230
  Shares

Masana’antar kannywood ta kama da wuta sakamakon rikici da ya barke tsakanin manyan jarumai guda biyo wato Ali Nuhu da kuma jarumi Adam A Zango wanda har hakan takai ga zagi da cin mutunci.

An tsinkayi jarumi Adam A Zango yana kalaman zagi ta uwa ta uba a shafinsa na Instagram ga jarumi Ali nuhu, hakanan ma ya kara wallafa wannan zagi a shafinsa na Facebook a safiyar yau litinin.

Jarumi Adam Zango yayi ikrarin cewa Ali nuhu ne ya sanya yaranshi domin suyi mishi zagi na cin mutunci, a sabili da hakane ya yanke shawarar hawa kafafen sadarwa na zamani don shima ya rama zagin da aka yi masa.

Har yanzu dai jarumi Ali nuhu bai maida martani ko yace wani abu ba dangane da ikrarin Adamu zangon, sai dai magoya bayansa sun maida martani a inda wasu ke kokarin nusar da Zango kan cewa abinda yake ba daidai bane.

A kwanakin bayane dai jarumi Adam Zango ya bayyana cewa shine bahaushen da yafi kowanne bahaushe suna a duniya wanda hakan ya jawo cece-kuce.


Share this on:
 • 230
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  230
  Shares