Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Fitaccen jarumin wasan kwaikwayon Hausa Adam A.Zango ya gargadi magoya bayan shi da yan uwanshi kan mayar da martani mai tayar da rigima kan wadanda ke zagin sa a shafukar sada zumunta.

Jarumin ya bayyana hakan a shafin sa na instagram tare jawo hankalin kanne da abokanai har ma da yaran shi na yin hani wajen tayar da hayaniya.

“DAGA YAU DUK WANDA YA KARA RIGIMA KO HAYANIYA AKAN AN ZAGENI KO AN ZAGI IYAYENA A CIKIN KANNE NA, ABOKAINA DA YARANA….ALLAH YA ISA BAN YAFE MASA BA” kamar yadda ya rubuta.

Idan ba’a manta ba a kwanan baya jarumin da abokin aikin sa kuma kuma babban jigo na masana’antar kannywood Ali Nuhu sun samu sabani ยป wanda ya tayar da iska tsakanin mabiyan su.

Duk da cewa jaruman sun sulhunta kansu bayan kokarin da wasu masu ruwa da tsaki na masana’antar kannywood suka yi na neman kawo karshen rigimar dake tsakanin su wannan bai hana wasu daga cikin mabiyan su cigaba da yi ma juna kalaman batanci ba.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •