Shahararren mawaki kuma shahararren dan wasan kwaikwayo na barkwanci Ado Isa wato Ado Gwanja ya bayyana cewa dukan da aka mishi da sanda a makon da ya gabata kan kuskure ne.

an daki Ado Gwanja

Ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo tare da Nasiru horo dan mama inda ya bayyana cewa anzo kaima wani duka ne sai aka kuskure aka same shi a gefen ido wanda hakan yayi sanadiyar kumburar gefen idon nashi.

Ya kara da cewar masoyanshi su kwantar da hankalinsu kan wannan dan karamin abu da ya faru tunda gashi har ya warke, kuma komai zai cigaba da tafiya daidai.

Ado Gwanjan yana kuma kara jaddadawa masoyanshi dake Niamey Niger cewar yana nan zuwa da sallah don gudanar da wasa…..

Ads