A yaune Shugaba kuma wanda ya assasa kafar sadarwar zamani ta facebook wato Mr Mark Zuckerberg ya ziyarci birnin Lagos don kaddamar da wani muhimmin aiki kan cigaban sadarwa a Nigeria.

Wannan shiri da suke shirin kaddamarwa anyi masa lakabi da Express Wi-fi wanda wani tsari na data mai saukin gaske gami da kyawu matuka ga ma’abota harkar yanar gizo a yankuna na karkara da birane.

Facebook dai ya fara kaddamar da express Wi-fi ne can a kwanakin baya a kasar India, inda zuwa yanzu kuma ya yanke shawarar kawo shi yankin Africa don muma mu amfana ta hanyar hada gwuiwa da kamfanin Cool link da kuma wasu yan kasuwan.

Wasu daga cikin tsarukan data na Express Wifi
Ana sa ran express Wifi zasu rika siyar da 100mb daily akan N40 , 750mb / 7days akan N270 da kuma 3GB / 30 days akan N1600 kacal.

Shin kuna ganin wannan zai kawo mana sauki wajen amfana da yanar gizo a kasata Nigeria?