Jama’a barkanku da wannan lokaci na yammacin wannan rana ta Alhamis, fatan kuna cikin yanayi na jin dadi. A wannan lokaci kuna tare da Deendabai wanda zai yi muku bayani kan ko cewar “factory reset” a android yana goge duka bayanan kan waya?

Mukan yi wa wayoyinmu factory reset musamman a yayin da muka zo sayar dasu don tabbatar da cewar mun goge duk wasu bayanai namu misalin su Facebook account, google, whatsapp, email da sauran wasu muhimman abubuwa da baza muso ace mun barsu suna yawo a duniya ba. Sai dai kuma kash, factory reset bai wadatar ba wajen goge bayanan kan waya.

Binciken da wasu masana suka gudanar a can baya ya nuna cewar factory reset da mafi yawanci masu amfani da wayoyin android ke yi baya goge ainihin kundin bayanansu gaba daya, illa iyaka dai kawai yana goge su ne a zahiri amma a badinance bayanan na nan kan kwakwalwar wayar kuma za’a iya gano su ta hanyar yin amfani da wasu dabaru da masana sirrin bincike a waya kan iya.

Wannan tsaiko dai an fi danganta shi da wayoyin android masu tsarin manhajar V2.2 zuwa 4.3 wanda masana suka alaqanta hakan da sakaci daga kamfanin Google da kuma masu habbaka tsarukan wayar android din.

Akwai wani ma’ajiyi na bayanan duka wasu al’amura da suka taba wanzuwa akan wayar da ake kira da Master token wanda da shi ne za a iya amfani wajen dawo da duka wasu bayanai ko wasu abubuwa masu muhimmanci da aka taba ajiye wa akan wannan wayar. Ba mamaki ka ce zakayi reset din wayar ka don ka goge duka bayanan ka dake kai, amma yana dakyau kasani cewa za a iya dawo da bayanan naka bayan da ka riga da ka goge ta hanyar amfani da shi wannan master token din.

Ta yaya zan iya goge bayanan kan waya ta baki daya

A magana ta zahiri babu tabbacin cewa in ka goge kayayyakin ka daga kan wayar ka shikenan sun tafi kasantuwar wannan master token din da aka gano amfanin shi wajen dawo da duka bayanan baya na kan wayar.

Mafita itace ka tabbata ka yi encrypting din wayar ka kafin kayi factory reset dinta a yayin da ka bukaci saida wayarka. Encryption yana tsare waya ta hanyar boye wasu muhimman abubuwa tare da tsare su da tsatstsauran password ta yanda babu wani da zai iya yin wani abu dasu face kai.

Yanda zakayi encrypting din shine kaje Setting > Security > Encrypt phone. Amma fa ka sani cewar dole wayarka ta kasance akan chaji yayin gudanar da encryption din domin aikin yakan dau lokaci mai tsawo wanda idan aka sami matsala zai iya goge maka wasu files din, saboda da haka kar kace Deendabai bai fada maka ba. Bayan encryption din sai ka goge duk abubuwan da kake son gogewa sannan sai ka siyar..

Yana dakyau ka sani cewa in kayi encrypting din wayarka to za a bukaci kasa password a duk lokacin da ka kunnata.

Wannan itace yar takaitacciyar shawara ga masu amfani da wayoyin android a yayin da suka bukaci siyar dasu..