Share this on:
 • 27
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  27
  Shares

Jarumar wacce ta shirya shirin
Sarauniya, Kukan Kurciya da Mairo da dai wasu fina-finai daban tace yin fim sana’a ce kamar sauran sana’o’i kuma yadda ma’aikata ke zuwa masana’antar su haka suma ke zuwa daban farfajiyar su.

Hannatu Bashir jarumar kannywood da tayi fice a harkar shirya fim ta bayyana cewa tana dab da yin aure kuma idan Allah ya kaddarar da faruwar hakan zata dakatar da harkar fim domin bada muhimmanci wajen kula da iyalin ta.

A hirar ta da wakilin BBC Hannatu tana mai cewa “Ko wace mace tana son ta ganta a gidanta kuma tana kula da iyalen ta. Idan ina da mijin yanzu idan nayi aure, ka gan zan fita da safe zuwa wajen aiki wa zai kula dashi? Idan kuma na fara tara yaya wa zai kula mun dasu?.

Ka gan ya zama dole in hakura da daya. Kuma harkar fim dinmu ba a iya kano kadai muke yi muna iya zuwa wasu garuruwa muyi.
Ina da miji zai barni in tafi wani gari inje inyi kwana biyar zuwa goma wajen daukar fim? kaga abu ne mai kamar wuya.

“Ni daia zaman aure ya fiye mun kudin da zan samu kuma ya fiye mun komai da komai ma” .

Hannatu wacce ta kwashi sama da shekaru bakwai a dandalin nishadantarwa na Kannywood tayi karin haske game da zargin da ake yawan yi ma yan fim na cewa su yan iska ne. A cewar ta mafi yawanci mata dake aikata hakan bata-gari ne wadanda suke fakewa da cewa su yan fim ne.

Tace mafi yawanci katin bogi suke yawo dashi da yin karya cewa su yan fim ne domin idan aka bibiya sau da dama jaruman basu san da zaman su ba a masana’antar.

Tace irin hakan yana faruwa sosai kuma mafi yawanci ire-iren yan matan da zarar an kama su sai su fake da cewa suna fim tare da nuna katin shaida na karya.


Share this on:
 • 27
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  27
  Shares