Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Yayin da 2017 ke neman karewa, ga jerin jarumai biyar na masanaántar Kannywood da suka samu tasiri cikin shekarar.

Kannywood 2017

Shafin Pulse ya fitar da wannan sunaye bisa la’akari da irin rawar da suka taka da kuma nasarorin da suka samu wajen tantance su cikin abubuwan da suka duba akwai nuna basira da gwaninta tare da nasara da aka samu a gidajen kallon fim (sinima) da yanayin yadda ki’imar jarumin ya samu daukaka a masana’antar shirya fina fina na kasar baki daya.

Ga jerin jaruman kamar haka;

1. Ali Nuhu

Sarkin Kannywood kamar yadda ake masa lakabi ya cigaba da nuna basirar sa a farfajiyar shirya fina finai imma masana’antar kannywood ko ta Nollywood duk ya samu damar haskawa bana.

Fitaccen dan wasan ya shirya tare da bada umarni a shirin ”Mansoor” wanda ya samu karbuwa a wajen dimbin masu bibiyar fina-finan hausa.

Banda haka jarumin ya haska a fina-finan nollywood kamar ”Hakkunde” wanda ita ma jaruma Rahma Sadau ta fito a ciki, ”Banana Island Ghost” da ”Ojukokoro”.

2. Maryam Yahaya

Sabuwar jaruma Maryam Yahaya ta shigo kannywood da kafar dama domin tun fitowar ta a cikin shirin “Mansoor” ta samu karbuwa, wanda hakan ya bata damar fitowa a fina-finai daban daban.

Jarumar zata kara fitowa a cikin wani sabon shiri tare da abokin aikin ta na ”Mansoor” watau Umar M. Shereef. Film din “Mariya” wanda zai fito kasuwa nan bada jimawa kuma wanda kamfanin Maishadda ya dauki nauyin shiryawa shine wanda wannan jaruma zata kara haskawa.

3. Rahama Sadau

Hakika jaruma Rahama Sadau ta taka rawan gani a harkar fim bana domin yan Nijeriya dama sun yaba kwarewarta yayin da ta fito a cikin wasu fina-finai kamar irinsu “Hakkunde” , ”Tatu” , “Accidental Spy” , “Ajuwaya” da “Sons of the Caliphate” na masana’antar nollywood.

Shirin fim na farko da jarumar ta dauki nauyin shiryawa da kanta “Rariya” ya samu kyauta na zama shirin fim da yayi fice a masana’antar Kannywood na mujallar city people.

4. Maryam Booth

Bana Jaruma Maryam Booth ta haska a fina-finai daban daban na kannywood da nollywood masu kayatarwa. Ta fito cikin shirin “Hakkunde” da “Rariya” har ma a cikin ”Sons of the caliphate”

5. Aminu Sheriff Momo

Bana dai shekara ce wacce tauraron jarumi Aminu Sheriff ke haskawa ganin yanda ya taka muhimiyar rawa a dandalin nishadantarwa ta kannywood. Banda fim jarumin yana gabatar shirye-shirye mabambanta masu kayatarwa a gidan telibijin na Arewa24.

Mawuyaci ne a rasa ganin shi a cikin manya manyan fina finan hausa da suka fito cikin 2017. Kwarewar sa da nuna gwanintar sa ya sanya mujallar city people ta karrama shi da kyautar gwarzon shekara na farfajiyar kannywood na bana.

-Pulse Hausa


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •