Share this on:
 • 9
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  9
  Shares

Fitacciyar tsohuwar jarumar fina-finan Hausa Kannywood wato jaruma Muhibbat Abdussalam ta bayyana cewa babu mahalukin da ya isavyasan tsakanin ta da mijinta ballantana har yayi yunkurin shiga tsakanin su.

Jarumar dai wacce take auren babban darakta Hassan Giggs wacce itama take mazaunin darakta a fina-finan Hausa ta wallafa wannan sako a shafinta na sadarwar zamani na Instagram inda ta bayyana cewa tana zaman lafiya da mijinta.

“Wooooooooohoho duniya mutane basa rasa abin fade. Idan kina zaman lafiya da mujin ki ace kin mallake shi, idan kuma kuna yawan fada ace baki da tarbiya.”

“To magulmata masu zuwa lahira da kokon danbu, Hassan Giggs da Muhibbat dashen Allah ne, se kuyi hakuri, Dan kuwa babu wanda ya isa ya san tsakanin mu, shi yasa ba da kowa nake kawance ba saboda sharrin masu hassada, su shigo jikin ka su cuce ka.”

“Ni dai ga dogara da Allah. Gani nan bari”.


Share this on:
 • 9
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  9
  Shares