Share this on:
 • 18
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  18
  Shares

A kwanakin baya ne dai Philomina Chieshe ta
sanar cewa maciji ne ya shiga ofishin su kuma ya hadiye N36M na daga kudin shiga na hukumar.

Sai dai wannan labarin nata ya sha bambam da wanda ta bayyana ma hukumar EFCC yayin da ake tuhumar ta kan laifin wawure kudin hukumar.

A wata takarda da hukumar ta fitar wanda jaridar TheNation ta wallafa, ita wannan ma’aikaciyar tace wani babban ma’ aikacin hukumar ne kuma wanda take karkashi sa ne ya al’mumdahana da kudin.

A cewar ta ma’ aikacin mai suna Mista Samuel Sale Umoru ya amshi kudin ne domin aiwatar da wasu ayyukan hukumar ko kuma na kan sa.Tace dai bisa umarnin sa take cire kudin kashi-kashi daga na’urar cire kudi na bankin ta.

Hukumar EFCC ta tabbatar da faruwar hakan inda ta bincika ko an samu hakan daga bankin ta.
Bisa ga wannan sabon labarin da ta fitar, hukumar ta garkame Samuel Sale Umoru domin cigaba da bincike kan zargin da ake.

Wannan labarin maciji wanda ya hadiye kudi ya janyo cece-kuce inda jama’a da dama suka yi ta mamakin faruwar hakan. Daga ciki kuwa har da dan majalisar dattawa Shehu Sani wanda har sai da ya kai agaji hedikwatar hukumar inda ya kai masu masu farautar macizai.


Share this on:
 • 18
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  18
  Shares