Akalla mutum 140 suka mutu bayan da wata babbar mota da ke dauke da man fetur ta fara ci da wuta a wani gari da ke gabashin Pakistan, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Gobara Ta Kashe Akalla Mutum

Rahotanni sun ce wasu gungun mutane ne suka isa wurin da tankar ta fadi don su diba man da ke tsiyaya. Ana cikin haka ne sai gobarar ta tashi.

Masu aikin ceto sun shaida wa BBC cewa tana iya yiwuwa wani mashayin taba sigari ne da ke kusa ya haddasa gobarar.

“Wani cikin mutanen da ke wucewa ne ya kunna sigari kuma daga ne sai mummunar al’amarin ya faru,” in ji Jam Sajjad.

Firai ministar Kasar Nawaz Sharif ya katse ziyarar da yake yi a Landan saboda faruwar al’amarin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Pakistan APP ya bayyana.

Pakistan ba ta hanyoyi masu kyau kuma ana yawan samun tukin ganganci daga bangaren direbobi wanda hakan ya ke ci gaba da jawo hadurra a kasar.

Ads