Akalla ma’aikatan Google mutum dubu biyu ne(2000) suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da dokar da shugaban kasar Amurka Donald Trump yasa wacce ta haramtawa wasu kasashen musulmai guda bakwai shigowa kasar. Kasashen da abun, ya shafa sune Syria, Iraq, Iran, Libya, Yemen, Sudan da kasar Somalia.


Photo: express.co.uk

Shugaban babbar kafar sadarwar zamani ta Facebook Mark Zuckerberg shine wanda ya fara fitowa yayi Allah wadai da wannan mataki na Trump. Mark Zuckerberg har wayau ya kasance shugaban kungiyar masu tarbar yan gudun hijira ta Fwd.us.

Ma’aikatan Google daga sassa daban-daban na fadin kasar ta amurka sun gudanar da jerin gwano don nuna kyamarsu ga wannan hukunci na shugaba Trump. Wasu daga cikin guraren da aka gudanar da wannan zanga-zangar sun hada da New York, San Francisco, Seattle da sauran wasu muhimman gurare.

Daga cikin wadanda suka halarci wannan zanga-zanga akwai CEO na kamfanin Google wato Sundar Pichai tare da daya daga cikin wadanda suka assasa Google wato Sergey Brin. Inda Brin din ya bayyana cewa shima ya shigo America ne a matsayin dan gudun hijira a lokacin da ake tsakiyar rikici a can kasarsu.

Suma anasu bangaren kamfanin Twitter sun nuna rashin goyon bayansu ga wannan mataki na Donald Trump inda suka bayyana cewa gamayyar baki mabanbanta addinai ne suka hadu wajen gina twitter saboda haka basa goyon bayan a kori ko a hana dan wata kasa shigowa Amurka.

Kamfanin Apple, Uber da sauran wasu manyan kamfanonin fasahohin zamani suma sun nuna rashin goyon bayan su ga wannan mataki.

Muma anan arewamobile mun yi Allah wadai da wannan tsatstsauran mataki da Donald Trump ya dauka. Bama kyama ko gudu kowa.