Kamfanin shirya fina-finai na GG production karkashin masana’antar shirya fina-finai ta kannywood na shirin fito muku da wani kayataccen wasan kwaikwayo mai suna Gudun tsira wanda aka kiyasta cewa zai lakume kudi har kimanin Naira Miliyan Goma a yayin gudanar da shi kamar yadda producer na film din wato Nuhu Abdullahi ya bayyana.

Daga cikin yan wasan da zasu fito a wannan kayataccen shiri akwai manya-manyan jarumai irinsu Ali Nuhu, Nuhu Abdullahi, Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, da sauransu. Daraktan wannan film dai ba wani bane illa zakakurin darakta Falalu A Dorayi.

Wannan shiri zaiyi nuni ne ga yadda mutane ke wauta da ababen hawa akan tituna da kuma irin hadurran dakan auku a sanadiyyar hakan. Sannan producer na shirin ya bayyana cewa hakan zai sanya Direbobi da yawa su ankara da irin hadarurrukan da ke tattare da irin tukin ganganci da wasu daga cikinsu keyi.

Film din wanda za’a fara haskawa a karshen wannan wata na Maris da muke ciki (28th March 2017) wanda za’a yi shi a bisa tsarin shirya fina-finai na duniya domin da zarar an gamashi za’a nunashi a gidajen Cinema cikin gida zuwa na kasashen ketare.

Idan baku manta ba a karshen shekarar 2015 ne masana’antar ta kannywood ta fidda wani film mai suna Hindu wanda Hassan Gigs ya bada umarni. Anyi ittifakin cewa film din hindu ya lakume kudi kusan miliyan ashirin(N20m) a yayin daukarsa.