Share this on:
 • 43
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  43
  Shares

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tallafawa Jawahir Rabilu Musa diyar marigayi Dan Ibro da kayan daki.

Iyalen marigayi sun nuna godiyar su bisa wannan hidimar da mai girma gwamnan jihar Kano yayi masu.

Auren dai an daura shine jiya asabar tare da angon ta Saleh Isa a garin Danlasan karamar hukumar Wudil dake jihar Kano.

Jawahir Rabilu Musa ita ce babban diyar tsohon fitaccen dan wasan kwaikwayo Marigayi Rabilu Musa Ibro wanda ya rasu ranar 9 ga watan disamba na 2014.

Daurin auren dai ya samu halartar mutane da yawa daga masana’antar Kannywood da kuma wajen masana’antar.


Share this on:
 • 43
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  43
  Shares