Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Hon. Aminu Bello Masari ta fitar da sanarwar cewar za ta mayar wa ma’aikatan lafiya na kananan hukumomi da tsarin albashin CONHESS da aka dakatar a watannin baya.

Wannan sanarwa dai ta fito ne daga babban mai magana da yawun gwamnan a kafar sadarwa ta zamani Abdulhadi Ahmad Bawa wanda ya wallafan labarin a shafinsa na Facebook.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau a gidan Janar Muhammadu Buhari, fadar gwamnatin jihar Katsina, bayan ya amshi rahoton kwamitin da gwamnati ta kafa domin tantance ma’aikatan da suka cancanci amsar wannan tsarin albashi. Ya kara da cewa wadanda aka tantance ne kadai za a mayar mawa kuma biyan zai hada har da ariyas na watannin da suka gabata.

Tun farko dai a nashi jawabin, shugaban kwamitin Alhaji Salihu Maigari Danjuma mni, ya bada rahoton cewa Kwamitin wanda ya kunshi har da shuwagabannin kungiyoyin kwadago, ya tantance ma’aikata har 8,640 wanda kunshi;

1. 4,811 da suke aiki a asibitoci

2. 2,015 na bangaren samar da ruwa da tsabtar muhalli.

3. 1,038 na bangaren aikin gona

4. 776 na bangaren Ilimi da walwalar jama’a.

Haka kuma sun sami Ma’aikata 1,056 wadanda suka rika amsar wannan alawus ba bisa ka’ida ba,a saboda haka sun bada shawarar a mayar dasu kan tsarin albashi irin na sauran ma’aikata. Haka kuma sun bada shawarar da a inganta tsarin kula da duba asibitocin tare da Ma’aikatan domin kauce ma fadawa cikin irin wannan matsalar nan gaba.

Kwamitin kuma ya bada shawarar cewa duk wani mai dauke da takardar kammala karatu (Statement of result) wadda ta kai tsawon shekara 10 to lallai ne ya kawo Satifiket (Certificate) kafin a yarda da zaman shi Malamin lafiya.

Idan ba a manta ba a can baya wasu daga cikin ma’aikatan lafiya sun shiga cikin halin kunci matuka sakamakon janyen CONHESS da gwamnatin jahar tayi.

Tura wa abokanka….