NCC sim card reg

Hukumar kula da harkokin sadarwa NCC haramta yin rajista layi(SIM card reg) da ake yi a kasuwanni, bakin tituna, kiosks, wajajen taruka da sauran makamantan su, inda suka buka ci masu yin su kasance a mazauni na dun dun dun kuma ya kasance domin aiwatar da rajistar layin kadai.

Shugaban kwamitin dabbaka doka da oda na hukumar NCC Salisu Abdu ne ya fitar wannan sanarwa ga yan jarida jiya a Abuja biyo bayan wasu mutane uku da jami’an hukumar suka kama suna yi ma mutane rajista a bakin titi.

Hakan ya biyo bayan matsalar da hukumar tace tana fuskanta wajen bin diddikin bayanan layukan mutane, inda basa samun damar samun cikakkun bayanan da suke bukata. Hasali ma wasu layukan akan yi musu rajista a siyar dasu haka nan.

Jami’in ya kara da cewar tun watan Nuwamban bara ne gwamnatin tarayya ta umurci da a sanarwa kamfanonin sadarwa cewar su dakatar da wakilan su dake aikin rajistar layi daga cigaba da yin rajistar a wuraren da suka hada da Kasuwanni, bakin tituna, kiosks, guraren shakatawa da sauran su.

Hukumar ta bayar da sharadin cewar dole ne duk wani mai yin rajistar layi ya kasance a ginan nen mazauni na dundun dun wanda ke dauke da alamomi da shaidun cewa nan gurin aiwatar da rajista ne sabanin yan rumfuna da ake tsirawa a bakin tituna da kasuwanni haka zalika ma masu kiosk da sauransu.

Daga yanzu akwai hukunci mai tsanani da hukumar ta yanke akan duk wanda aka kama yana yin rajistar layi ba a guri da aka tanada musamman don hakan ba, za’a chaji mutum tarar kudi ta Naira million biyar (N5million)