Fitacciyar jarumar wasan Hausa ta kannywood Rahama Sadau ta dora wasu hotuna guda 4 a shafinta na instagram da twitter a wannan rana ta Valentine wato yau 14 ga Fabrarirun ko wacce shekara. Akan kira wannan rana da “Valentine day”.

Valentine day dai ya samo asali ne daga kasar Rome inda wani abu ya faru tsakanin sarkin Romawa na lokacin mai suna Claudius na biyu II yasa aka kama gami da garkame wani mutum mabiyin addinin kiristanci mai suna Valentinus, wanda daga bisani sarkin yasa aka kashe shi saboda da samunsa da laifin saduwa da yarsa(sarkin) wacce ta kasance makauniya da aka kawo don yan rinka koya mata karatu..