Rahama sadau ta amsa gayyatar da wasu jaruman Hollywood; akon da Jeta amata sukayi mata don su yi wani wasan kwaikwayo mai taken “The American King” wanda zasu shirya shi a wasu birane na kasar Amurka , Senegal South Africa da Nigeria.

Idan baku mance ba a kwanakin baya ne kungiyar masu tace fina-finai MOPPAN ta kori Rahama sadau daga kannywood bayan wani hoton video na waka tare da classiq inda ta nuna wasu dabi’u da basu dace da kundin tsarin kannywood ba.

A yanzu haka dai rahama sadau din tana birnin Los angeles don gudanar da wannan film din wanda za’a dauka a watan December mai zuwa. Ga ragowar hotunan nan a kasa: