Shahararriyar yar wasan kwaikwayon nan ta kannywood, Rahama Sadau ta maida martani dangane da wani audio na jita-jita da aka rinka yadawa a kafar sadarwa ta WhatsApp kan cewar wai zata bar addinin Musulunci sakamakon tayi da aka yi mata da wasu miliyoyin dalolili, da kuma samun matsayin shiga masana’antar wasan kwaikwayo ta Hollywood.

Ta bayyana cewa wannan zance ne da bashi da tushe ko makama wanda kuma an kirkire shi ne don a bata mata suna, inda ta nuna damuwa matuka sannan kuma ta bukaci jama’a da suyi watsi da wannan recording na audio da ake yadawa. Ta kara da cewar sana’arta baza ta shafi addininta ba ballantana ma har ace zata sayar da imaninta wa wasu yan dalolili.


Idan zaku iya tunawa, a can bayane jarumar ta fito a wani faifan Bidiyon waka tare da mawakin hiphop Classiq wanda hakan ya jawo kakkausar suka a gareta inda daga bisani hakan ya janyo MOPPAN Ta kori Jarumar daga kannywood wanda sanadin hakan ne ta samu gayyata zuwa masana’antar fina-finai ta Hollywood dake kasar Amurka.

“Abin ya kona min rai matuka, musamman ma ta yadda har wasu manyan malamai suka yarda da wannan jita-jitar da aka rinka yadawa kuma suka yi amfani da ita wajen suka ta ba tare da sunyi bincike don tabbatar da sahihancin labarin ba, wanda hakan ya harzuka yan uwa da abokan arziki. Abisa wannan dalilin ne naga ya zama wajibi na fito na yiwa jama’a bayani. “

Ni Rahama Sadau inaso in shaidawa al’umma gami da jaddada musu cewar wannan zancen da ake yadawa akai na karya ce mara tushe da aka kirkiro don a bata mun suna, saboda haka ina kira ga masoya na da su yi watsi da wannan jita-jitar.

Ta kara da cewar” in baku manta ba, Akon wanda yake musulmi ne kuma dan asalin kasar Senegal ya fuskancin irin wannan kalubalen daga kafafen yada labarai na can kasar ta su.

Tura wa abokanenka dake Facebook, Twitter, WhatsApp da sauransu.