A kwanakin bayane kamfanin apple ya fitar da sanarwar fitar da sabuwar wayarsu kirar iPhone 7 plus.

Kawo yanzu wayar ta fantsama ya zuwa gurare da yawa na kasuwannin duniya inda ake sayar da ita ba kakkautawa dukda kasancewar tana da tsada matuka.

A halin da ake ciki, wayar iPhone 7 ta riga da ta iso Nigeria da kuma kasar Kenya. Yan Nigeria zasu iya samun wannan wayar a kasuwar hada-hadar kayan kimiyya ta zamani wato jumia shopping inda suke sayar da ita akan farashi N473,700 kacal.

Daga cikin abubuwan da wannan waya take dasu akwai:
• 128GB storage
• Water resistivity (ko ta fada ruwa na tsawon minti 30 baza tayi komi ba)
• Camera mai kyau(akalla 12mp )
Da sauransu…

Ko zaka iya cire zunzurutun kudi har kusan Naira dubu dari biyar ka sayi waya kamar wannan?

Tura wa abokai….