Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Shahararren jarumin nan na Kannywood wanda aka fi sani da Sarki, Ali Nuhu ya bayyana cewa wasu daga cikin manyan jariman masana’antar na da niyan tsayawa takara a zaben 2023.

Ali ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da shafin BBC, sai dai jarumin ya bayyana cewa wasu daga cikin su sun taba takara a baya.

“A gaba ma yanzu, yana daga cikin irin kudurin da muke da shi, wasu daga cikinmu su fito a 2023 su tsaya takara,” cewar jarumin.

Jarumin ya kara da cewa jarumai irinsu Abba El-Mustapha da Nura Hussaini duk sun taba tsayawa takara a zabukan Najeriya.

Da aka tambaye shi ko su wane ne suke da burin shiga harkokin siyasa ka’in da na’in, sai ya ce: “Ba zan iya fadar suna ba yanzu, saboda abu ne da ke kan matakin shirye-shirye”.

An tambaye shi cikin raha ko wata rana za a ga fasta dauke da hoton Ali Nuhu yana takarar shugaban kasa, sai ya kyalkyale da dariya yana cewa: “Ah haba! Gaba daya?”

Daga bisani ya ce “Allah dai ya tabbatar mana da alheri amma dai gaskiya muna da wadannan shirye-shirye.”

An kara matsawa da tambayar ko jarumin shi da kansa yana da sha’awar tsayawa takara a zaben Najeriya? Tauraron ya ce “A gaskiya a yanzu ba ni da sha’awa”.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •