Kamar dai yadda babbar kafar nan ta yanar gizo wato forbes da ke wallafa jerin sunayen mutanen da suka fi arziki a duniya daga lokaci zuwa lokaci ta saba, a shekarar bana sun fitar da sabon list dauke da sunayen mutanen da suka fi kudi a duniya, inda wasu daga cikin yan Nigeria suka sami damar shiga.

aliko dangote
Alhaji Aliko Dangote

Ba tare da na cika ku da surutu ba, bari in zayyano muku jerin
sunayen mutane goma (top ten) dake kan gaba wajen tsabar dukiya a Nigeria.

10 Oba Otudeko

Oba Otudeko shine mutum na goma a cikin wannan jeri. Attajirin shine keda kamfanin Honeywell. Ya shahara wajen samar da Flour, haka zalika babban dan kasuwa ne a bangaren man fetur da gas, baya ga Wadannan kuma, Oba Otudeko ya shahara sodai wajen dakon kaya ta jiragen ruwa.

Tarin dukiya: dala miliyan dari shida da hamsin ($650million )

9Jim Oviah

Mutum na tara a wannan jeri, shine wanda ya assasa Zenith bank kuma yake da babban kaso da yakai goma cikin dari(10%) na ribar hada-hadar kasuwanci dake gudana a wannan banki. Jim Oviah bai tsaya a Zenith bank kadai ba, domin ko ya kasance shi ke juya harkokin kamfanin sadarwa na Visafone.

Tarin dukiya : Dala billion daya ( $1billion)

8 – Orji Uzor Kalu

Tsohon gwamnan jihar Abia kuma mutum na takwas a wannan jeri. Shine ya assasa Slok holdings, kamfanin da ya shahara wajen harkar shigo da kaya daga waje, harkar mai, kasuwanci da sauransu. Kalu ya fara kasuwanci tun yana dan shekara sha tara (19), biyo bayan korarsa da aka yi daga jami’ar da yake karatu a lokacin saboda samunsa da laifin tada tarzoma.

Tarin dukiya : Dala billion daya da digo daya ($1.1billion
)

7 – Tony Elumelu

Chairman na Bankin UBA Africa. Shine ya assasa kamfanin Transcorp and Heirs Holdings.

Tarin dukiya: dala billion daya da digo daya billion daya da digo hudu ($1.4billion
)

6 – Abdussamad Isyaka Rabiu

Mutum na shida a kudi a Nigeria. Abdussamad shine shugaban shahararren kamfanin nan na BUA wanda ya shahara a bangaren harkar kayan abinci irinsu Taliya, Sugar haka zalika bangaren kayan gini irinsu siminti da sauran harkokin safarar kayan amfanin yau da kullum.

A shekarar 2015 ne dai Abdussamad ya kafa tushen ginin kamfanin hada siminti na kimanin dollar miliyan dari shida ($600 million) a jahar Edo.

Tarin dukiya: Dala billion daya da rabi ($1.5billion
)

5 -T. Y Danjuma

Mutum na biyar a kudi a Nigeria. Ya rike mukamin shugaban sojojin Nigeria daga 1975 zuwa 1979. Shine kuma Chairmnan na Athlantic petroleum.

Tarin dukiya: dala billion daya da digo bakwai $1.7billion
)

4 – Folorunsho Alakija

Itace mace da tafi kowacce mace kudi a Nigeria. Tana harkar kayan kyalekyale, harkar mai, buga tagardu da sauransu.

Tarin dukiya: dala billion biyu da digo daya ($2.1billion
)

3 -Femi Otedola

Shugaban kamfanin Zenon oil and gas da kuma kamfanin forte oil plc.

Tarin dukiya : dala billion biyu da digo uku ( $2.3billion
)

2 – Mike Adenuga

Mutum na biyu a kudi a Nigeria. Yana da hannun jari a bangaren mai, gas da kuma bangaren harkokin sadarwa. Mike Adenuga shine ke da kamfanin sadarwa na Globacom Nigeria (Glo), haka zalika kuma shine chairman na Conoil.

Tarin dukiya : dala billion goma da rabi ($10.5billion
)

1 – Aliko Dangote

Mutum na daya a kudi a Nigeria, na daya a Africa sannan kuma wanda yafi kowanne bakar fata kudi a duniya. Aliko dangote shugaban kamfanin dangote group ya kasance mutum na ashirin da hudu (24) a duniya a shekarar 2016, amma yanzu ya sauko zuwa sama da na 100 sakamakon matsin tattalin arzikin bara da aka shiga.

Tarin dukiya: Dala billion sha biyu da rabi ($12.5billion
)

Wadannan sune mutane goma yan kasuwa da suka fi kowa tarin dukiya a Nigeria kamar yadda shafin forbes ya wallafa..

Marubci: DEENDABAI
arewamobile.com