A kwanakin bayane nayi wani rubutu akan sanarwar da kamfanin whatsapp ya fitar ta cewar Whatsapp zai daina aiki akan wadansu wayoyi ciki ko harda wayoyin blackberry z10, window phones da kuma wasu kananun wayoyin android.

whatsapp-zai-dena-aiki

Kamfanin ya fitar da sanarwa a yau din nan cewar daga ranar 31 ga wata December na bana wato karshen shekarar 2016 kenan, whatsapp zai denayi a cikin wadannan jerin wayoyin:
-Blackberry(harda blackberry 10)
-Wayoyin Java
-Symbian
-Windows phone
-Wayoyin android kananu irinsu 2.0,2.1..
Da sauran kananun wayoyin da acan da ke iya bude whatsapp din.

whatsapp-zai-dena-aiki

Wannan mataki dai da kamfanin whatsapp din ya dauka ya samo asali ne daga kokarin da kamfanin yakeyi na ganin cewar ya sanya wasu sabbin tsare-tsare da zasu kara kawatar da shi application din nasu.

To shawara ga masu mutuwar son wadannan wayoyi da aka ambata a sama shine suyi kokari su canza zuwa wayoyin da zasu iya tafiya da zamani har su saba dasu kafin cikar wannan wa’adi.