Jama’a barkanku da wannan lokaci, fatan alkhairi gareku baki daya gami da fatan kuna cikin walwala da koshin lafiya wajen samun damar karanta wadannan bayanan da zan zayyano a nan gaba cikin rubutu na.

amfanin-zogale-ga-dan-adam

Yau shafin arewamobile zai yi bayani ne kan wasu alfanu da zogale wanda ake kira da Moringa Oleifera a harshen turanci ke da su ga lafiyar dan adam. Ina fatan zaku iya jurewa wajen karanta dukkan bayanan.

Zogale ko kuma ince ganyen zogale ya kasance wani ganye ne dake dauke da sinadarai masu matukar amfani ga lafiyar mutum wadanda dan adam ke bukatarsu sosai wajen gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum..

Bincike da masana sukayi ya nuna gami da tabbatar da cewa zogale yana maganin sama da cututtuka dari uku(300). Daga cikin manyan cututtuka da yake magani sun hada da ciwon hawan jini, ciwon sugar, cancer gami da kashe tsutsotsin ciki..

Yadda masanan suka bada shawarar a rinka amfani dashi zogalen shine ta hanyar shanya shi ya bushe (amma fa ba acikin rana ba) sannan sai a daka shi sannan sai a rinka shanshi a cikin ruwan tea (shayi) ko kuma a zuba shi a ruwa hakanan.

Karin magungunan da yakeyi a jikin dan adam sun hada da wadannan:

– Yana taimakawa wajen lafar da wasu matakai da ke kaiwa ga haddasa ciwon zuciya da ciwon sugar.

– Yana taimakawa wajen magance hatsarin kamuwa da ciwon cancer.

– Yana taimakawa wajen gyaran fatar jikin mutum, ma’ana yana kara taimakawa kyawun fata wajen sanyata tai haske gami da sheki.

– Yana dauke da Vitamin A, wanda kowa yasan amfanin vitamin A wajen kara lafiyar Ido.

– Zogale yakan taimaka wajen sarrafa abincin da mutum yaci cikin sauki..

– Yana dauke da sinarin calcium wanda sinadari ne mai amfani sosai wajen kara kwarin kashi a manya, sannan kuma yana taimakawa yara wajen karin kwarin hakora.

– Yana taimakawa wajen tafiyar da al’amuran tsaro ko kuma kariya na jikin dan adam daga cututtuka

– Binciken da masana sukayi ya tabbatar da cewar shan ruwan zogale yana dakyau ga mata masu shayarwa, wajen kara yawan madarar dake dauke a cikin nono domin shayarwa.

Ina fata da yan bayanan da na zayyano muku a sama zasu dan amfane ku kadan dangane da muhimmanci cin ganyen zogale ko kuma shansa a cikin ruwa.

Idan da mai wani karin bayani ko kuma wasu karin alfanu akan abinda na zayyano to sai ya ajiye mana su ta hanyar yin commenting a nan kasa.

Ku tura wannan labari wa abokanku dake facebook, twitter whatsapp da sauransu ta hanyar danna share buttons da ke kasa..