Katafaren kamfanin kasar China da ya shahara wajen kera wayoyi ya bada sanarwar shirye-shiryensa da yake na bude masana’anta da za’a rika kera wayoyin kamfanin a nan Nigeria.

Mataimakin manajan hada-hadar kasuwancin kamfanin a Nigeria mr. Attai Oguche ne ya bayar da wannan sanarwa a Lagos a yayin da suke bikin fitar da sabuwar wayar Phantom 6 plus, inda yace a yanzu haka ma har sun sami filin da zasu gina wannan kamfani.

Mr Oguche ya kara da cewar a yanzu haka Ethiopia ce kadai kasar dake da kamfanin kera wayoyi na techno dukda dai cewa akwai wasu manyan ofisoshi na hada hadar kasuwanci a sassa daban-daban na Africa musamman a Nigeria , Kenya da Tanzania.

Ya bayyana cewa saboda muhimmancin kasuwancin da suke da shi a Nigeria yasa kamfanin ya yanke shawarar bude reshen hada wayoyin a nan.

Wannan zai kasance babban cigaba ga yan kasa baki daya , tunda hakan zai sama wa matasa aikin yi sosai haka zalika hakan zai taimakawa masu kasuwancin siyarda irin wadannan wayoyi na kamfanin Tecno…

Tura wa abokai..