Share this on:
 • 20
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  20
  Shares

A Daren jiya 7 febuary ne aka kawo karshen takaddamar da ta barke tsakanin fitattun jarumai biyu Ali Nuhu da Adam A. Zango, wanda wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar fim suka shiga tsakanin su don ganin a sasanta su.

An yi sasancin ne a ofishin Shugaban Hukumar Tace finafinai Isma’il Na’Abba Afakallahu. Sauran wadanda suka shiga aka yi sasanci da su sun hada da Sani Sule Katsina, Falalu A. Dorayi, Nura Hussaini
.

Hakan ya kawo karshen takaddamar da ta barke tsakanin mabiyan su wadanda suka rika duddurwa juna ashariya a shafukan instagram tsakanin magoya bayan Ali Nuhu da na Adam A. Zango.

Falalu Dorayi ya rubuta a shafin sa tare da wallafa hoton su tare bayan kammala zaman neman sasanci.

“Alhamdulillah.
Alhamdulillah.
Alhamdulillah.

An kammala Ganawa cikin alkairi. Ali Nuhu da Adam A Zango Allah ya kara hada kawunanmu.

Allah ka tsare Film industry daga dukkan masifu. Ya bamu zama lfy. Ku kuma Ismail Naabba_Afakallah da Sani Sule da Hussain Nura Allah ya biya ku. Ameen.” Kamar yadda ya rubuta.

Suma dai jarumai sun wallafa sakamakon zaman da suka yi da jiga-jigan a shafukan su.

Wannan ya nuna cewa komai ya warware tsakanin su kuma za’a cigaba daga inda aka tsaya wajen nishadantar da jama’a.


Share this on:
 • 20
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  20
  Shares