Da alama dai rikicin da ake ta yayatawa dake tsakanin manya kuma shahararrun jaruman nan mata na masana’antar Kannywood watau Rahma Sadau da Nafisa Abdullahi ya zo karshe komai ya wuce.

Rikicin Rahama Sadau da Nafeesa Abdullahi

Mun dai fahimci hakan ne ta dalilin wani rubutu da jaruma Rahma Sadau tayi a shafin ta na dandalin sada zumunta na Facebook inda take taya abokiyar sana’ar tata watau Nafisa Abdullahi murna dangane da wani muhimmin ci gaba da ta samu.

A haka saidai muce komai yana gab dayawuce tunda har daya ke iya taya daya murna kan wani cigaba daya samu.

ko me zakuce…..