ministan mai

Karamin Ministan man fetur na kasa wato Dr. Ibe Kachikwu ya tabbatarwa da jama’a cewa suna sa ran matsalar man fetur da kuma dogon layi da akeyi a gidajen mai zasu kau daga gobe laraba zuwa jibi.

Ya bayyana hakan ne wa manema labarai bayan kammala taron da sukayi da kungiyar lura da farashin man fetur ta kasa (PPPRA) yau a Abuja.

kachikwu yace: “Muna fatan matsalar layi da ake fama dashi a gidanjen mai zata kau daga gobe a manyan garuruwan Abuja da kuma Lagos.”

ya kara da cewar zuwa karshen mako suna sa ran matsalar ta kau a wasu garuruwan irinsu Kano, Katsina, Sokoto, Port Harcourt da kuma Warri..

Ya kara tabbatar wa da yan Nigeria cewa yana nan kan alkawarinsa da ya dauka na ganin sun magance wannan matsala data dabaibaye kasa cikin kankanin lokaci..

Allah ya kawo mana saukin wahalhalun da muke ciki..

Ku tura zuwa ga abokanku na facebook da twitter da kuma whatsapp…