Shinkafa (Scientific name: Oryza sativa )

Shinkafa na daya daga cikin kayan amfanin gona da aka fi amfani dasu a sassa daban-daban na duniya musammam ma ta bangaren abinci. Baya ga masara da rake, shinkafa ta kasance hatsi da jama’a suka fi nema a duniya.

Yankin Asia ya kasance yankin da yafi kowanne yanki zarra wajen noman shinkafa a duniya sakamakon matakai na zamani da suka dauka wajen inganta harkar. Daga cikin kasashen dake kan gaba a wannan yanki akwai; China, India, Indonesia, Vietnam, Thailand, Bangladesh, Myanmar, da Philippines wanda suke samar da akalla ton miliyan dari shida (600million ton) a shekara wato kusan kaso tamanin da bakwai (87%) na shinkafar da ake amfani da ita a duniya baki daya.

Daga karin kasashe da suka yi suna sosai wajen noman shinkafa akwai Brazil, Japan, Pakistan, Cambodia, America, Korea ta kudu, Egypt,
Nigeria, Nepal, Nigeria, Madagascar, Mozambique, Uganda da sauransu.

A yankin nahiyar Africa, arewamobile tayi kokarin zakulo muku kasashe biyar dake kan gaba wajen noman shinkafa a yankin.

1.Nigeria

A shekarar data gabata ne dai Nigeria ta kasance ta dawo kan gaba a sahun kasashen da ke noma shinkafa a wannan yanki na nahiyar Africa Sannan kuma ta goma sha hudu (14) a duniya. Hakan ba zai rasa nasaba da alwashin da sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka na ganin ta inganta harkar noma a kasar don samar da isashshen abincin da za’a ci harma a siyarwa makota.

Hasashe na nuni da cewar a yanzu haka kasar na samar da akalla ton million 7 na shinkafa daga sassa daban-daban na kasar a noman shekara guda, inda kuma ake sa ran samun cigaba a shekaru masu zuwa.

Dukda yawan shinkafar da kasar ke nomawa, Nigeria ta kasance kasar da tafi kowacce kasa shigo da shinkafa daga kasashen waje don amfanin yan kasar. Ana sa ran cewa yawan shinkafar da ake shigowa da ita zai ragu sosai duba da yadda gwamnati ke kokari wajen ganin ta habaka noma a kasar.

2.Egypt

Egypt itace kasa ta biyu bayan Nigeria wajen noman shinkafa a wannan yanki namu na nahiyar Africa. Alkaluma dai sunyi nuni da cewar kasar ta Egypt na samar da akalla ton miliyan shida (6 million) a duk shekara, wanda hakan yai daidai da yawan bukatar yan kasar. Ma’ana dai ita kasar ta Misra tana noma isashshiyar shinkafa don amfanin yan kasar. Amma fa kada ku manta da cewar Nigeria tafi Egypt yawan al’umma.

3. Madagascar

Kasar Madagascar itace ta uku a jerin kasashen dake da arzikin noman shinka a Africa. Kasar takan noma akalla ton miliyan 5 wanda yakai akalla kaso casa’in da shida (96%) na shinkafar da yan kasar ke bukata.

4. Mozambique

Kasar Mozambique itace kasa ta hudu a cikin jerin kasashen da sukafi noma shinkafa a nahiyar Africa. Yawan shinkafar da kasar ke nomawa bai wuce ton dubu dari shida ba. Shinkafar da kasar ke nomawa bata wadatar da yan kasar, a sabili da haka ne suke shigo da shinkafar da yawa daga kasashen ketare.

5. Uganda

Kasar Uganda ma sukan dan tabuka wajen noman shinkafa musamman ma wacce suke amfani da ita. Hasashe yayi nuni da cewa kasar na samar da akalla ton dubu dari uku na shinkafa a shekara.

Wannan shine dan takaitaccen rubutu da ni Deendabai zan iya yi dangane da noman shinkafa a nahiyar Africa. Idan anga wani gyara ko kuma wani kuskure a cikin rubutun za’a iya sanar dani ta comment box dake kasa ko kuma ta lambar waya ta 08135658217

Marubuci:

DEENDABAI
arewamobile.com