Akalla mutum takwas ne aka tabbatar mutuwar su a sanadiyyar wani rikici daya biyo bayan batanci ga ma’aiki da wani dalibi yayi a makarantar Audu Gusau polytechnic dake talatan-mafaran jihar Zamfara.


Gwamnan Jihar Zamfara

Shi dai wannan lamari ya faru ne yau litinin inda wasu daga cikin daliban sukayi gangami suka fara dukan dalibin inda Wani mutum mai suna Tajuddeen yayi yunkurin cetonsa ta hanyar daukarshi a mota da zummar ya kaishi asibiti.

Matasan dake gurin sun fusata bisa wannan mataki da Tajuddeen din ya dauka inda suka tafi gidansa suka cinna mashi wuta wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutum takwas dake cikin gidan.

Tuni dai rundunar yan sandan jihar ta kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe 7 na yammacin yau Zuwa 7 na safiyar gobe.