Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Kannywood wato jaruma Ummi Zee-zee ta bayyana a shafin ta na sadarwar zamani na Instagram cewa ko yau ta mutu to ta gode ma Allah bisa irin daukakar da yayi mata a harkokin ta na rayuwar yau da kullum.

Wannan rubutu dai data wallafa a ranar Alhamis 15th February, 2018 wacce rana ce ta zagayowar ranar haihuwar ita wannan jaruma, wanda a sabili da haka ne ta wallafa wannan sako.

Jarumar ta kara gode ma Allah bisa bukatunta da ya biya mata, sannan kuma bisa azurta ta da yayi fiye da yadda take nema, hakanan kuma ya kareta fiye da yadda take kare kanta.

Sai dai kuma an samu wadanda suka soki jarumar bisa irin shigar data yi a hoton data dora tare da wannan sako dama wasu daga cikin hotunan da ta dora a kafar bisa dalilin cewa hoton ya saba da addini jarumar, hakanan ma da al’adar yankin da jarumar ta fito.

Wasu daga cikin masu bayyana ra’ayin kuma sun nusar jarumar ne kan cewar babbar daukaka a gareta shine ya kasance cewa tayi aure ta huta wanda shine cikar mutuncin ya mace.

Wasu kuma sun jefe ta da maganar cewa tayi tsufa da yawa inda har ta kaiga tana mayar musu raddi da zagi.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •