Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  

A jiya alhamis ne dai wata babbar kotu dake zamanta a Nomansland dake cikin birnin Kano ta baiwa kwamishinan yan sanda umarnin ya kamo mata fitacciyar jarumar nan ta Kannywood Hadiza Aliyu wacce aka fi sani da Hadiza Gabon bisa kin amsa kiran kotu da tayi a farko.

Alkalin kotun Muntari Dandago ya kuma baiwa kwamishinan umarnin a tuhumi jarumar bisa karar da Mustapha Naburaska ya shigar akanta kan dukan da tayi wa jaruma Amina Amal a kwanakin baya.

Ya zuwa yanzu dai jarumar bata ce komai ba dangane da wannan umarni na da wannan kotu ta bada akanta.

A kwanakin baya ne dai aka tsinkayi wani bidiyo a shafukan sadarwa na jaruma Hadiza Gabon ta tutse jaruma Amina Amal tana dukan ta bisa kiran da tayi mata da yar madigo a shafinta na Instagram wanda hakan ya janyo cece kuce a cikin jama’a.


Share this on:
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •