Share this on:
 • 122
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  122
  Shares

-Sarki Ali Nuhu ya nuna goyon bayansa ga shugaba Buhari


A lokacin da zaben 2019 ke kara karatowa, mutane dama wasu kungiyoyi nata nuna goyon bayansu ga manya-manyan yan takarar shugabancin kasa; Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar.

A makon nan ne dai muka wallafa jerin sunayen yan wasan kwaikwayo na Hausa da suka nuna goyon bayansu ga shugaba Buhari da kuma jerin wadanda ke goyon bayan atiku. Jarumi Ali nuhu tare da karin wasu jarumai basu bayyana ra’ayinsu ba a wannan lokacin.

A yaune jarumi Ali Nuhu ya bayyana goyon bayan shi dari bisa dari ga shugaba Buhari. Ya bayyana hakane ta shafinsa na Instagram inda ya dora hoton shugaba Buhari tare da rubuta “My president”.

A makon daya gabata ne dai uwar gidan shugaban kasa Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta karrama jarumi Ali Nuhu tare da wasu manyan jarumai a Abuja.


Share this on:
 • 122
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  122
  Shares