Shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya dakatar da sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal tare da Shugaban hukumar leken asiri ta kasa (NIA) Ambassador Ayo Oke.

Shugaban ya bada umarnin a gudanar da bincike kan badakalar kudaden kula da yan gudun hijira da suka bata a yankin gabashi da ya sha fama da rikicin ta’addanci na yan Boko haram.

Buhari ya kara da umartar ayi bincike kan makudan kudaden da aka gano a birnin Ikko(Lagos) wanda shugaban hukumar leken asirin ya alaqanta kansa da su.