Share this on:
 • 39
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  39
  Shares

Ko ka kasance ma’abocin son rike babbar waya kirar android mai dauke da muhimman abubuwa masu yawa amma kuma kana so ta kasance akan farashi mai rahusa duba da yanayin halin karancin kudi a hannu? arewamobile.com ta kawo muku jerin wayoyin android har guda goma sababbin fitowa, dauke da abubuwan da kuke bukata akansu kuma akan farashin da bai kai ko ya wuce dubu ashirin da biyar ba(N25,000).

Bawai wayoyin android kala goma bane kadai da zaku iya samun su a farashi kasa da dubu 25, akwai su da yawa fiye da duk yadda kuke tunani. Sai dai mun zabo wadanda muke ganin suna tafiya da zamanin da ake ciki, wadanda zasu iya gwabzawa da manyan wayoyi masu tsada.

Abubuwan da shafin arewamobile.com ya duba wajen zabo muku wadannan wayoyi masu saukin farashi sun hada da: Karfi da kyawun Camera, zubin manhaja, Girma ko fadin screen, karfin battery, saukin kudi, girman ma’ajiyar kan waya(internal storage) dama sauran wasu abubuwan da bamu zayyano a cikin wannan rubutu ba.

Ba tare da na cigaba da dogon surutu ba, bari in kaiku kai tsaye ga wadannan wayoyi, bayanan su da kuma farashin su..

1. Cubot R9

Wayar Cubot R9 waya ce mai inganci sosai musamman ta bangaren girma da kyauwun Camera dinta ta gaba data baya, inda matsayin ta bayan yakai 13 Mega pixels, ta gaban kuma 5 Mega pixels.

Baya ga nan kuma, fadin ma’ajiyar kan waya wato “internal storage” yakai 16GB sannan kuma kwakwalwar aiwatar da ayyukan waya wato RAM nata yakai 2GB so babu maganar ta rika yin jinkiri(slow) a yayin da kake amfani da ita.

Wayar Cubot R9 na kan manhajar android Nougat wato version 7.0 na android. Sai dai kuma karfin batirinta 2600mAh wanda ba dole bane ya gamsar da mai amfani da ita, musamman in ya kasance ma’abocin hawa online a koda yaushe.

Ga takaitaccen bayanin ta a kasa

kudin Cubot R9

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
7.0 Nougat 5.0 inch 13MP back, 5MP front 16GB + 2GB RAM 2600mAh

N19,599

2. Leagoo KIICAA POWER

Kamar wayar Cubot R9, wayar Leagoo ma an inganta ta da abubuwa da dama, kamar ma’ajiyarta mai matsayin 16GB da kuma 2GB RAM.

Sai dai kuma Leagoo bata kai R9 karfin camera ta baya ba, domin kuwa karfin camera din da aka yo ta dashi shine 8 Mega pixels.

Sai dai wayar Leagoo an kero ta da battery mai inganci, domin kuwa yafi na Cubot R9. Karfin batirin wayar Leagoo shine 4000mAh.

Ga karin takaitaccen bayanin ta a kasa

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
7.0 Nougat 5.0 inch 8MP back, 5MP front 16GB + 2GB RAM 4000mAh

N20,990

3. Motorola Moto C

Kamfanin Motorola suma sun fito da tasu wayar mai suna “Moto C” wacce ke aiki akan manhajar android version six wato “marshmallow”.

Duk da dai ba dole bane ya kasance ta gamsar da mai amfani da ita, kamfanin sunyi kokari sosai wajen inganta ta.

Ga karin bayabai a kasa

nawa ne kudin Moto C

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
6.0 marshmallow 5.0 inch 5MP back, 2MP front 8GB + 1GB RAM 2350mAh

N20,999

4. Oukitel C8

Wayar Oukitel C8 kusan zubinsu daya da wayar Cubot R9 da nayi bayani a farkon rubutu na, sai dai wannan ta darar ma Cubot da karfin battery da kuma fadin screen.

Itama Oukitel tana aiki ne akan manhajar Nougat (android 7). Sannan kuma tana da camera ta baya mai karfin 13 Mega pixels ta baya 5 Mega pixels.

Ma’ajiyar ta 16GB da kuma RAM da yakai 2GB, sannan sai battery mai karfin 3000mAh.

Ga karin bayanai a kasa

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
7.0 Nougat 5.5 inch 13MP back, 5MP front 16GB + 2GB RAM 3000mAh

N23,300

5. Bontel R10

Wayar Bontel R10 tafi duka wayoyin da muka zayyano karfin battery, domin ko karfin batirinta ya kai 6000mAh wanda zai yima duk mai yawan hawa yanar gizo dadi.

Baya ga karfin battery, wayar Bontel R10 an inganta ta da Camera ta baya da ta gaba masu karfin 13 Mega pixels da kuma 8 Mega pixels a tsare.

Sai dai ita Bontel, 8GB ne akanta da kuma 1GB RAM. Amma duk da haka waya ce mai kyau kuma mai rahusa.

Ku duba karin bayani a kasa..

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
7.0 Nougat 5.5 inch 13MP back, 8MP front 8GB + 1GB RAM 6000mAh

N23,329

6. itel P12

Itel P12 ta yi tashe a shekarar bara. Tana da battery mai inganci sosai. Sai dai kuma kamfanin basu inganta ta da camera mai kyau sosai ba.

Idan muka duba bangaren ma’ajiya (internal storage da RAM) to zamu ga kamfanin itel basu yi kokari ba, domin kuwa 8GB ne akanta da kuma RAM 512MB.

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
6.0 marshmallow 5.0 inch 5MP back, 2MP front 8GB + 512GB RAM 5000mAh

N23,500

7. Tecno WX3

TECNO ma ba’a barsu a baya ba wajen kero waya mai sauki da kuma inganci. WX3 ta fito a shekarar bara dauke da dan madaidaicin battery da camera iri daya, wato 5 Mega pixels gaba da baya.

Duba bayanin kasa

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
7.0 Nougat 5.0 inch 5MP back, 5MP front 8GB + 1GB RAM 2500mAh

N23,600

8. iMose GiDi

Wannan wata wayace da take da battery mai inganci sosai. Sannan kuma tana da camera ta baya mai dan madaidaicin kyawu.

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
6.0 marshmallow 5.0 inch 8MP back, 2MP front 8GB + 1GB RAM 4500mAh

N24,500

9. Homtom S16

An inganta Homtom S16 da battery, camera da kuma ma’ajiya mai girma.

Homtom tana da Kyau sosai.. Duba bayanan ta a kasa

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
7.0 Nougat 5.5 inch 8MP back, 5MP front 16GB + 2GB RAM 3000mAh

N23,900

10. Fero Power

Fero POWER na dauke da battery mai kyau sosai. Sannan tana da dan matsakaicin ma’aji ga kuma Camera ta baya.

Zubin Manhaja (android version) Fadin waya Karfin Camera Ma’ajiyar kan waya(Storage) Karfin battery Farashi
6.0 marshmallow 5.0 inch 5MP rear, 2MP front 8GB + 1GB RAM 3600mAh

N24,990

Wadannan sune iya wayoyin da muka tsakuro muku bayanan su da farashin su a kasuwannin yanar gizo da kuma shagunan siyar da wayoyi yare da bayanin yanayin inganci ko wacce daya daga ciki.

Zaku iya duba shagon siyar da wayoyi na Jumia.com.ng don kara darjewa. Haka nan kuma zaka iya ziyartar shagunan siyar da wayoyi mafi kusa dakai don zabar taka.

Marubuci: Deendabai
CEO, arewamobile.com.


Share this on:
 • 39
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  39
  Shares