A ranar larabar nan data gabata ne dai majalissar dokokin jahar Katsina ta fitar da sanarwar tsige kakakin majalissar ta Aliyu Sabiu Muduru gami da nada sabon kakaki Abubakar Yahaya Kusada wanda ya maye gurbinsa a nan take.

Abubakar Yahaya Kusada -  Aliyu Sabiu Muduru

Yan majalissa 23 cikin 34 dake wakiltar kanan hukumomin jahar Katsina ne suka rattaba hannu akan goyon bayan kudirin tsige muduru inda 11 daga cikinsu kuma suka ki goyon bayan kudurin kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Daga cikin wadanda basu sa hannu akan kudurin tsige mudurun ba akwai : Aliyu Sabiu (Kakaki mai barin gado), Abduljalal Runka, Bishir Mamman, Garba Yau,Nasir Yahaya, Mustapha Abdullahi, Umar Gambo, Salisu Hamza da Abubakar Sulaiman.

Wannan mataki dai ya zone a yayin da ake cikin gudanar da zaman majalissa kamar yadda aka saba kwatsam sai shugaban masu rinjaye na majalissar Hambali Faruk ya miko ma Aliyu Muduru takardar tsige shi.

Biyo bayan hakan ne aka ga tshohon kakakin tare da wasu daga cikin magoya bayansa suka fice daga zauren majalissar inda daga bisani aka hange su a gidan shugaban jamiyyar APC na jaha.

Bayan tsigewar ne aka umarci mukaddashin kakakin majalissar Shehu Tafoki daya hau gurbin kakakin gabanin a nada sabon shugaba.

Menene ya janyo aka tsige Muduru ?

Maganganu da yawa nata kaikawo akan ko menene musabbabin tsige Aliyu Muduru daga kujerar sa. Jama’a dai suna zargin cewa shi Mudurun ya samu matsala ne da wasu manyan jam’iyya wadanda suke mazaunin iyayen gidansa ne, wadanda ake ganin ta dalilin su ne ya samu wannan matsayi.

Dama dai tun farkon hawan shi kan wannan kujera anyi ta yamadidi ganin cewar akwai wadanda suka fishi gogewa da cancantar zama a wannan mukami domin akwai dokar majalissar da ta yanke cewar sabon zuwa majalissar bazai iya zama kakaki ba sai dai wanda yake a matakin zuwa na biyu ko na uku.

Idan akabi ta wannan dokar dake hana bakon zuwa zama kakaki a wannan lokaci mutum 4 ne kawai ke da damar tsayawa takarar kujerar; Yameel Dutsi, Shehu Tafoki, Abdullahi Mahutu da kuma Magaji Rumah. Muduru ya sami damar darewa wannan kujera biyo bayan soke wannan doka data haramta masa damar zama.

Tun bayan nadin nashi ne dai wasu daga cikin yan majalissar dama wasu jiga-jigan gwamnati keta adawa da shi, har ya zuwa lokacin da aka tsige shi. Sai dai kuma masu sharhi na ganin cewa matsalar da ya samu da wasu iyayen gidansa ne daga sama ta janyo mashi hakan.

Akwai rahoto da ke nuni da cewar Aliyu Muduru yana kokarin hada gungun siyasa na kansa wanda hakan ka iya zama barazana gasu iyayen gidan nasa, wanda hakan ne ake kyautata zazon ya jawo masa asarar mukamin nasa.