Share this on:
 • 3
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  3
  Shares

Manhajojin wayar android, sunan su, matakinsu da kuma lokacin da aka fiddo su.

Tun bayan da shahararren kamfanin fasahar zamanin nan wato Google ya sayi gami da mallakar manhajar android a shekara ta dubu biyu da biyar (2005) aka cigaba da habbaka gami da inganta tasirinta ya zuwa wannan lokaci da muke ciki.

A duk cikin sabuwar manhajar da akan fitar ana kara sanya wasu abubuwa don inganta kirar wayoyin da ke fitowa a wannan lokacin.

Ga jerin zubin Manhajojin da kuma sunayen da ake musu lakabi.

1. Android version 1.0 an fitar da ita a ranar talata, 23rd September, 2008.

2. Android version 1.1 wacce akai wa lakabi da “Petit Four”. An sake ta a ranar Litinin, 9th February, 2009.

3. Android version 1.5 Ana Kiran wannan manhaja da “Cupcake”. Ta fito a ranar Latinin ta 27th April, 2009.

4. Android version 1.6. An yi mata lakabi da “Donut”. Ta fito a 15th September, 2009.

5. Android version 2.0 – 2.1. Ana kiranta “Eclair”. Ta fito a 26th October, 2009.

6. Android version 2.2 – 2.2.3. Lakabin ta shine “Froyo”. An sake ta a May 20th, 2010.

7.Android version 2.3 – 2.3.7. Wannan itace “Gingerbread”. Ta fito a December 6th, 2010.

8. Android version 3.0 – 3.2.6. Lakabinta “Honeycomb”. An saki a February 22nd, 2011.

9. Android version 4.0 – 4.0.4. Sunanta “Ice Cream Sandwich”. Ta fita a October 18, 2011.

10. Android version 4.1 – 4.3.1. Itace “Jelly Bean”. An saki a July 9th, 2012.

11. Android version 4.4 -. 4.4.4. Ana mata lakabi da “KitKat” an sake ta October 31st, 2013. Wannan na daga cikin manhajojin da jama’a suka fi amfani da su sosai a yanzu.

12. Android version 5.0 – 5.1.1. Lakabin ta shine “Lollipop” ta fito a November 12th, 2014.

13. Android version 6.0 – 6.0.1. Ana kiran zubin wannan manhaja da “Marshmallow” ta fito a October 5th, 2015. Wannan itace zubin manhajar da kaso mafi yawa na mutane suka fi amfani da ita.

14
. Android version 7.0 – 7.1.2. An lakaba mata suna “Nougat” ta fito a August 22nd, 2016. Yawancin sababbin wayoyin da suka fito a 2017 a kan wannan zubin manhajar suke.

15. Android version 8.0 – 8.1. Lakabinta shine “Oreo”. Oreo dai zubin manhaja ne da har yanzu ake kara inganta sa. An saki zubin wannan manhajar ga masu gwaji da kuma ingantawa a ranar Latinin, 21st August, 2017. Wasu daga cikin manyan wayoyi irinsu Google pixel, Nexus, Oneplus da wasu daga cikin wayoyin HTC sun sami wannan sabuwar manhaja.

Akwai yiwuwar wasu wayoyin irinsu Samsung Galaxy S8, S7, Note da sauran su su biyo baya wajen samun damar daga darajar manhajarsu zuwa Oreo…

Warning!! Copyright ©arewamobile.com.

Permission to copy this article is granted subject to appropriate credit given to www.arewamobile.com, the origin .


Share this on:
 • 3
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
 •  
  3
  Shares