A wani rahoto da gidan radiyon BBC Hausa ya wallafa, an gano cewa a yanzu haka kasuwar motoci dake Cotonou ta ja baya sosai sakamakon dokar da gwamnatin tarrayar Nigeria ta sanya ta hana shigo da motoci ta hanyoyin kasa.

Rahoton ya nuna cewa kaso chasa’in (90%) na masu siyan motoci a kasuwannin nasu sukan zo ne daga Nigeria. Masu sayar da motocin sun ce yanzu kasuwar ta ja baya kuma farashin motocin ya sauko, saboda faduwar darajar Naira da kuma rufe iyakokin da Nigeriar ta yi wadanda suka taimaka wajen rashin samun cinikin motocin.

A baya dai jiragen ruwa na sauke kwantenoni ciki da motoci kamar dubu goma a wata,amma tun bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da sabuwar dokar,jirage a gabar tekun Cotonou suka ja baya inda a sati bai fi a sauke kwantenoni hamsin ba.

Karancin masu sayen motocin ya sanya wasu
daga cikin masu wannan harakar rasa ayyukansu. Majalisar Dattawan Nigeriar dai ta bukaci gwamnatin kasar da ta janye wannan matakin da ta ce ya haddasa dubban ‘yan kasar sun rasa aikin yi.

-BBC HAUSA